3 years and counting (a harshen hausa)

image

Yau tabbas babbar rana ce a gare ni, yau nake cika shekara uku (3) a industry. Sheraka uku (3)! Wow!!
Tun daga farko nasan cewa in har ina son bunkasa, farin jini da karbuwa a industry din nan dole na yarda da kai na, nasa kwazo, na kuma dauki wannan sana’ar tawa da muhimmanci. Komai mai yuwuwa ne in har mutum ya yarda da kansa. A kullum ido na budewa yake, a kullum koyan sabon abu nake a wannan industry din daga abokanan aiki, daga masoya da kuma yan uwa da abokanan arziki. Wayannan halaka da darusa na rayuwa a industry sun taimaka wajen zaman da ni Rahma Sadau din da ku ka sani.

Kulla yaumin ina godewa Allah da ya bani damar yin sana’ar da nake so, da kuma ya daukaka ni har duniya ta sanni. Bani da abin cewa sai dai na kara godewa Allah da ya daukaka ni ya kuma albarkatar min da wannan sana’ar tawa. Godiya ta
musamman ga kuma @RealAliNuhu dan yarda da yayi dani da kuma shawarwarin da ya cigaba da bani. Godiya kuma ga abokanan arziki da sauran jarumai na industry – jaruman kannywood nagode.     Ga iyayena, kanne na, yan uwa kuma ina godiya. Team dina kuwa – kun san kan ku ( ba sai na bayyana ku ba )- nagode….daga karshe godiya ga wayanda suka yi ni, wayanda suka girmama ni, wayanda suka sa sunan Rahma Sadau ya daukaka wato “FANS” dina. Ina muka babbar godiya. Duk kwazo na da gwaninta na saboda ku nake. Ina godiya kwarai da gaske, Allah ya bar zuminci ya kuma tabbatar da Alherinsa a gareku da mu gaba daya. Allah ya saka muku da alheri. Nagode. Rahama xxx

2 Comments Add yours

  1. Yakubu Yakson says:

    ALLAH YA KARA TAIMAKAWA AUNYY

  2. Shehu m kunu says:

    Allah ya taimaka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *