Wa ce ce Rahama Sadau (a harshen Hausa)

Sunana Rahama Sadau, nayi karatun Karamar Diploma, kuma a yanzu na koma makaranta inda nake  karatun babbar takardar shaidar Diploma ta kasa, wato HND Bangaren tsimi da tanadi. Na shiga  harkar fim a matsayin jaruma shekaru 3 da suka wuce bayan da na samu  gaiyyatar babban jarumi Ali Nuhu, inda aka bani wata babbar damar takawa, a matsayin babbar jaruma mace, a fim din “Gani Ga Wane”. Ni ma’abociyar kallon fina  finan India ce, hasali ma a nan ne na koyi   yadda ake  acting a film.

image

Jaruma Priyanka Chopra itace  gwarzuwa ta, kuma fina  finan ta, sun taimaka mini kwarai da gaske wajen kwarewa da zamowa jaruma da kowa ke so, saboda yadda take acting ne ke bani kwarin gwuiwa, da har a yanzu na zamo jaruma daya tankan da goma. A zuwa yanzu na taka rawa  a matsayin jaruma a fina  finai Sama da 64 na masana’antar  mu ta kannywood, kuma a halin yanzu ma ina  aiki kan wani shiri  mai suna “Rariya”. Na taka rawa da dama a nau’i daban daban na fina  finai,

Na zamo jaruma a fina finan soyayya, da na ban tausayi, da na ban tsoro, da fina  finan zamani  da dai sauransu. Fitowa mafi kyau da nayi, kuma nafi so shine lokacin da na fito a matsayin Jummala a film din “sabuwar soyayya”.

Na fito sosai a fina  finai da dama kamar dai yadda na Fada. Na fito a fina  finan kannywood dama na nollywood, akasari a matsayin jaruma sannan kalilan a matsayin makira.

Ina ganin  kwazo da hazaka ta, a matsayi na na jaruma, ya dogara ne kacokan akan kokarin da nakanyi na Ganin na nishadantar da masu kallo a kodayaushe. Nakan sanya  masu kallo su gamsu da sakon dake  cikin fina  finan dana fito, ta kokarin da nakanyi wajen gyara labari ta sigar  fita ta a matsayin jaruma.

Ni kaina  nakan yi bitar hazakata alokuta da dama, a yanzu nayi nisa kwarai da gaske a fannin  shiryawa da jaruntaka a film,  har ma wasu  Basa jin dadin gudanar da aikinsu ba ni.

Duk da dai mu jarumai bama gamsuwa da kwarewa ko kwazonmu, a kullum kokarin mu shine muga muna ci gaba ta hanyar  ribanya kwazon mu a aiyukanmu.

Kuma ko ni dinnan nakan bi duk wata hanya da zan inganta  fasahata don ganin  na kara zama fasihiyar yar wasa. Wani lokacin ma, zaunawa nakan yi  na dubi fina finan da nayi na baya, domin fahimtar inda  zan gyara.

Na kuma koyi  darussa da dama daga manyan  mu daraktoci, da jarumai, a Iya shekarun da nayi a masana’antar mu ta kannywood.

Nayi imanin cewar babban darasin da mutum zai koya a harkar masana”antar fina  finai, shine bada gudun mowa da zamowa kanwa uwar gami, akan  al’amuran mu’amulla da sauran jama’a.

4 Comments Add yours

 1. Aminu Aliyu Tukur says:

  Da kyau Rahamah Sadau fina finan ki suna qayatar da ni matuqa keep up with your acting activities

 2. Yakubu Yakson says:

  GASKIYA AUNTY ALLAH KAREKI

 3. Abba adamu says:

  Dakyau rahama haka mukeso fatanmu kifi haka,a gaskiya kina birgeni a film 100% domin koni bana kallonki film din hausa matuqar bake aciki a matsayin jaruma

 4. Abdulazeez Namadi says:

  Masha Allah. … Ina murna sosai da wannan turaka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *