SIYAN GIDAN RAHAMA SADAU A ABUJA ZUKI TA MALLAU. INJI RAHMA SAUDAU.

image

Shahararriyar Jaruma Rahma Sadau Ta karyata wani shafin yanar gizo mai suna www.hassankoch.wordpress.com akan kahru da yayi mata wai ta sai gidan Miliyoyin kudi a babban binnin tarayya abuja, Jarumar dai tace wannan karya ce tsagoranta domin bata san inda a kayi hakan ba a tattaunawar da tayi da Abban Aneesah ga yadda hirar nasu ya kasance.

Kannywoodtoday: Munji labarin abin Arziki ya samu na kin sai Makeken Gida a Binnin Tarayya Abuja?
Rahma Sadau: Wallahi yanzu haka na samu sakonnin murna akan wannan magana wanda har aka turomin da ta inda aka samu wannan labarin, amman gaskiyar magana karya ce, wallahi matsalan wasunku yan Jarida kenan basu bin cike akan abu sai kawai su buga amman in kaduba shi wannan shafi ma na wanine kawai dake neman kudi yayi blog dan ya dunga karya akan mu, kuma munyi magana da manager na da anemi koma waye daya cire wannan labari kuma ya karyata kanshi in ba haka zamu dauki mataki akai, domin wannan yayi kama da batanci.

Kannywoodtoday: Amman sai na ke ganin kaman abin arziki ne ya fada baki ganin ko yana maki fatan Alheri ne?
Rahma Sadau: Haba Abban Aneesah me yasa ga gaskiya kake son kauce mata, to meyasa kai baka buga hakan ba a shafinku sai da kanemi jin ta baki na, kaga wannan yana nufin kwarewa a aiki kenan, wannan fa irin masu neman kudin nan ne wanda suna son a dunga shiga blog dinsu kaman yadda na fada ma a baya amman kuma da karya da karerayi suke wallafawa, in ka kula dan yadda ya fara hakan nan gaba bakasan dame zai bullo ba kawai in ya karanta ya gani to ya gaggauta yin abinda mu kace in ba haka dokan kasa ta bani daman yin karansa dan bin hakkina dan nasan komin daran dadewa zamu hadu kuma mukama shi matukar bai karyata kansa ba kuma ya cire wannan batu. Bari kaji wani abu Abban aneesah ita fa karya ba inda take kai mutum ko kai an yarda da shafin ku ne saboda duk wani abu da kuke bugawa koda ko batunci ne to akwai gaskiya kuma sai kunbi don kuyi abinda turawa kece ma balancing, wato jin ta bakin wanda ake zargi danya kare kansa wannan ai itace ke nuna kwarewa, amman wannan irin abinda ke faruwa da Jaruman kudu ne ake son a kawo mana masana’antar mu to ba zamu amince dashi ba in kuma ya saba yima wasu abaya sun kyale to ni bazan kyale ba, kawai ina barci na da mun shari wani yasa wasu su fara farauta ta akan abinda ba gaskiya bane, sannan ka duba ka gani a wannan lokacin da zai irin wannan maganan, abin tambayar ma da wasu zasu fara shine ina na samu miliyoyin da har nasayi katafaren gida? kaga sai yasa afara min wani irin zargi wanda ko ba haka bane, daman gashi wasu jama’an na mana wani irin kallo, sannan kasan wani abu ne ma?

Kannywoodtoday: A’a sai kin fada
Rahma Sadau: Hoton dayayi amfani dashi Wani fans dina ne a Facebook dina officialrahmasadau yayi min designing a photoshop ya turomin har ina mishi dariyar nake tsokanina shi mukayi wasa da dariya dashi dan ni ina baiwa fans dina muhimmanci sosai nakanyi hira dasu lokaci lokaci in na samu dama, amman shine wannan da ban san da me zan kwatantashi ba kawai ya dauki hoton ya yake bayan ya jonani a wani gida wai ni Rahma Sadau na sai katafaren, Bari kaga original picture din a studio akayi kagani ko, kuma ai ya manta mutane sun waye kowa ya gani yasan jonani akayi a cikin gidan, hmmm to Allah ya kawo lokacin amman dai a yanzu ban sai ko wani gida ba ina cikin gidan iyayena ne tare dasu da ‘yan uwana.

image

Hoton Rahma Sadau da aka yanka kenan a ka daura ta a kata faren gida.

image

Hoton Rahma Sadau kenan a cikin gidan da aka sanya ta.

Kannywoodtoday: Daga karshe wani sakon garaki ga Masoyanki gaba daya, da ‘yan fim da kuma mu kanmu masu bibiyan lamuranku?
Rahma Sadau: Toh masoyana ina matukar jinjina a gareku domin kune nakai matsayin dana kai, dan da bazarku nake rawa, sannan ina kara bukatar addu’ar ku kamar yadda kuka saba, musamman ga wata mai daraja ya tsaya da fatan bazaku manta da taku ba Rahma ‘yar Sadau a cikin addu’o’in ku domin Allah ya kara yi min tsari da duk wasu makiyana na baiyane dana boye ya kuma kara daukaka maku ita, sannan ku jira fina-finai na masu fitowa nan bada jimawa wanda nasan zasu birgeku musamman fim dina RARIYA, kofa abude take ga dukkanin mai wata shawara gareni wanda zai kaini ga tudun mun tsira ina kara godiya a gare ku sosai, sannan kudunga tace duk wani labari da za’a fada akai na, kuma akwai shafina na yanar gizo https://rahmasadaublog.wordpress.com kuna iya dunga bibiyata donji wasu abubuwa akaina, sai kuma akwai kafofin yada labarai wanda ku kunsan sahihai ne dazaran sun buga labari ba akasan ba a Duniya ma an yarda dashi, sai www.kannywoodtoday.com.ng wanda nayi wannan hira dasu suna kokari amman fa bana fada dan in fasa muku kai bane (sai duk mukayi dariya) na fadi gaskiya ne, kuma in kuka chanja sai mu chanja ku mu daina mu’amala da ku, kuna iya bibiyansu akan duk wani abu dake faruwa a masana’antar fina-finan Hausa dan suna kokarin balancing din labaransu. Sannan mu kuma ‘yan fim da Allah yayi mu zauna tare muyi sana’a tare to mu gujewa hassada da cin dunduniyar abokin kasuwanci domin babu inda zai kaimu sai dai koma baya. Ku kuma yan Jarida masu bibiyan mu dan Allah ku dunga mana adalci a duk labaran da zaku buga akan mu, dan wannan na daga acikin abinda yasa wasunmu basu son yin hira daku jira kuke ko yaya ne mutum yadan saki layi a hira to fa kun samu caption din Labarin ku, to ku tuna fa damu daku dole akwai alaka mai karfi kar wannan alakar ta zama na batunci atsakani. Sannan kai hassankoch nasan ba danjarida bane dan daga blog dinka kowa zai fahinci haka dan fadin blog din naka ma kara tallata kane, Dan Allah Abban Aneesah kar kufadi sunan blog dinsa. Nagode Allah yabar zumunci.
Kannywoodtoday: Muma mun gode.

image

image

http://www.kannywoodtoday.com.ng/2016/06/siyan-gidan-rahama-sadau-abuja-zuki-ta.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *